Addua.org shafi ne na adduoi a cikin harshen hausa

Title

Addua.org ::: Barka da zuwa a gidan Addu'o'i -- Akwai Adduoi iri-iri anan| Adduar | Addu'ar | Mashlool | Kumayl | Aure | Matsala | Azumin Ramadhan | Karatun Qur'ani, Alqur'ani, Addua -- Adduar --- Hausa -- Addua a hausa -- hausa da addua

Description

Excerpted from the website description:

Shafin Addua na hausa domin amfanin Musulmi. Wannan shafin ya kunshi Addu'o'i iri dabam dabam kamar Mashlool, Kumayl, da sauran Addu'o'i duk a cikin shafin Addua.com

Da sunan Allah mai Rahama Mai Jinkai Karatu, nazari da binciken ayoyin Qura’ani mai girma abu ne wanda amfanin sa baya da iyaka. Hakika har yanzu ba’a iyakance sirrin dake cikin wannan Littafin mai daraja ba. Wadanda ke karatun Alqu’anin a ko wane lokaci zasu iya tabbatar da wannan domin a kullum ka karanta shi, to dole ne sai iliminka ya karu, ka kara sanin abinda daga baya baka fahimta ba. Karatun Alqurani a kullum baya gundurar da mutum sai dai a kullum yana kara ma mai karatun sa shaukin nazari akansa. Wace irin hasara ce ga wanda baya karatu da amfani da maganar Mahallicin sa? Wane uzuri ne ga mutum akan wannnan? Da mutane sun fahimchi Alqur’ani mai girma a hakikance, da sun wuce matsayin da suke a yanzu.

Ko wace sura, ko wace aya, kai ko wane harafi a cikin Alqur’ani akwai mala’ika ko mala’ikkun dake kula dashi, suna yi ma wannan surar ko ayar hidima ta musamman.

Akwai wasu surori da ayoyi a cikin wannan littafin mai daraja wadanda amfaninsu zai sanya mutum yayi mamaki matuka akansu. Wannan shine muradin wannan rubutun. Idan kuka biyo mu zamu baku bayanin wasu daga ciki gwaergwadon abinda muka iya debowa daga tekun ilimi.

Abin haushi shine, an bar dukkan wadannan mu’uzoji na Alqur’ani ba tare da amfani dasu ba. Ako wane gida, wajen ajiyar littafai, da makarantu zaka tarar da Alqur’anai sunyi kura saboda rashin amfani dasu. Wannan zai sanya Allah (SWT) ya tuhume mu akan wannan kuma bamu da wani uzuri na kare kanmu a gaban Manzon Allah (SAW).

External Links



Retrieved from "http://aboutus.com/index.php?title=Addua.org&oldid=29127285"